Muhimmancin Amfanin Saka Kamfe (Pant) Ga ‘Ya Mace - Android Pols


A cikin wannan video za ku ji muhimmanci dake tattare da saka pant ga mata, sai dai akwai mata da yawa wanda ba su damu da su saka pant a jikinsu ba har sai za su yi tafiya mai nisa, amma idan zaune suke a gida ba su damu su saka ba. 


Hakan yasa muka tattaro muku muhimmancin amfanin saka kamfe ga mata a kowane lokaci ba sai za'a fita daga gida ba. Ga wasu daga cikin amfanin saka kamfe kamar haka :


1- Yana hana Kura shiga gabanKi wanda Ke haifar da warin gaba.


2- Yana hana bushewar gaba wanda Ke haifar da KaiKayin gaba.


3- Yana Kare mutuncin mace yayin da hadari ya sameta Ko Kuma zuwan al’adar gaggawa  ya sameta.


4- Ga mace mai yawan farin ruwa a gabanta (discharge) sa Pant yana rage yawan futowanshi.


ldan da hali zaiyi Kyau ya zama mace tana da Panties da yawa Kamar 12 Saboda idan nata ya jiKe sai ta dinga canzawa, idan Kuma babu hali Ko Kina ganin Wahalar hakan to sai ki sami karamin towel ki aje a toilet dinki duk sanda kika yi tsarki sai ki goge/tsane gabanki da towel din Kafin ki mike tsaye kinga batun jikewar Pant zai ragu.


Haka kuma anaso mata su rika yin amfani ne da farin Pant a ko da yaushe saboda yana saurin taimakawa mace ta gane halin da gabanta ke ciki, misali colour discharge dinta ko unexPected menses zata zama alerted da wuri har ta dau mataki.


Don Allah a kula ke da rabuwa da Pant sai dai lokacin bacci. Sannan ku yi kokari ku koyawa yayanku yin hakan domin ku mata dole sai da kulawa da farjinku domin waje ne mai daraja kuma abin sha’awa amma ga wacce ta damu Kuma take kulawa da kanta.


Da fatan wannan fadakarwa za ta amfanar daku, kuma da fatan za'a Kula sosai wajen kiyaye lafiyar jikinku. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post