Daga Karshe Dai Adam A. Zango Ya Saki Matarsa Ta Shida Cikin Matan Da Yake Aure - Android Pols


A karshe dai shahararren mawaki kuma furodusa a masana’antar finafinai ta Kannywood, Adam A. Zango, ya saki matarsa, Safiya Umar Chalawa.


Safiya Chalawa ita ce matar Adam A. Zango ta shida da ya saka; ’ya’yansa bakwai, kowanne mahaifiyarsa daban, in banda biyu daga cikinsu. 


Jarumin ya sake ta ne shekara hudu bayan aurensu da aka daura a 2019 a Fadar Sarkin Gwandu a Jihar Kebbi.


Da haka ne Safiyya ta zama matarsa ta shida da ya saka a cikin shekaru 17 da suka gabata, daga 2006 zuwa yanzu.


Adam A. Zango, wanda ya yi tashe a Kannywood, yana da ’ya’ya bakwai, kowanne daga cikinsu mahaifiyarsa daban, in banda biyu daga cikinsu.


Tun a kwanakin baya dai akai ta cewa Adam A. Zango na dab da rabuwa da amaryarsa Safiya, wadda aka ji shi a wani bidiyo yana zargin cewa ta zabi kasuwancinta a kansa.


A cewarsa, hakan ne ya sa ba shi da wani zabi face ya hakura da ita, kuma idan ya rabu da ita ba zai kara yin aure.


Shin yaya kuke ganin wannan hukuncin da Adam A Zango ya dauka? Kuna ganinsa Zainab ki kara auren kamar yadda yai furucin hakan? 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post