Matakan Da Zaki Jawo Hankalin Tsohon Saurayinki Ya Dawo Miki - Android Pols
Wasu mazan suna rabuwa da wacce suke so ne ba domin ransu na so ba sai domin yadda masoyiyar tasa take yi masa.


Akwai 'yan matan da a koda yaushe hankalinsu na wajen namijin da ba aurensu zai yi ba. Sai sun wulakanta mai son su na gaskiya sai kuma wannan da suke so ya ware daga bisani kuma su soma kame-kame na neman wannan ya dawo.


Ga wasu matakan da za ki dauka bayan kinyi kuskuren koran mai sonki na gaskiya.

 

1: Ki Daurewa Zuciyar Ki Abunda Zaki Ji Ko Zaki Gani Wajen Dawo Da Soyayyar Ki Dashi.


2 : Kada Ki Soma Nuna Masa Bukatar Ki Kai Tsaye Da Farko.


3: Nuna Masa Ba Wai Dole Sai Kun Dawo Kaman Da Ba.


4: Soma Da Tura Masa Sakonnin Gaisuwa Amma Ba Kullum Ba.


5: Nemi Lokacin Da Zaki Iya Ganinsa Ku yi Magana. Amma Kada Ki Takura.


6: Ya Fahimci Cewa Ba A Son Ranki Abinda Ya Faru Ya Faru Ba Samo Wata Karyar Da Zaki Fadamasa Koda Ba Gamsuwa Zai Yi Na Abinda Ya Faru A Baya.


7: Tuna Masa Yadda Kika Nuna Masa So Da Kauna A Baya. Wanda Zai Yi Wuya Ki Cireshi A Ranki.


8: Tuna Masa Alkawuran Da Kuka Yiwa Juna Masu Mahimmanci A Baya.


9: Sanar Dashi Gaskiyar Yadda Kike Ji Tun Bayan Da Kika Gane Kuskurenki.


10: Jawo Hankalinsa Akan Muhimmancin Yafewa Mutumin Da Ya Gane Kurensa Ya Kuma Nemi Tuba.


Duk kuwa da ya danganta ne da yanayin da kuka rabu. Amma shi namiji a inda ya bambamta da mace shine bai kafewa akan kin yarda da sulhu muddin dai akwai soyayyar wanan macen a ransa.


Da farko zai iya miki tutsu akan bukatar taki. Amma da zaran ya fahimci kinyi nadama kuma wata ba ta maye gurbinki ba, zai sake baki dama.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post