Ko kunsan Cewa Ashe Ba Sha'awa kadai Ke Jawo Gaban mace Yin Danshi Ba - Android Pols


Ba maza kadai ke iya fahimtar lafiyar al'uransu ba. Kamar yadda muka yi darasi a baya na yadda duk safiya ko yadda gaban maza yake mikewa idan suna bacci.


Suma mata suna da hanyar da suke iya gane suna cikin koshin lafiya musamman ta bangaren farjinsu.


Sau tari wasu matan suna kokawa na yadda gabansu yake a jike a kullum. Wasu matan na daukan hakan tamkar wata lalurace ko kuma yawan jaraba ce na son Jima'i, sam abun ba haka yake ba a cewar masana. 

 

Shi gaban mace mai lafiya a kullum ana son ganinsa yana cikin naso da kuma danshi. Wannan ne yake tabbatar da mace na cikin koshin lafiya a bangaren al'auran ta, kamar yadda masana suka tabbatar.


Wannan ruwan da yake jika gaban mace ba yana nufin tana da karfin sha'awa bane. Sai dai ruwane da yake wanke duk wani abu mara kyau da zaran ya shigeta.


Da yake Allah ya halicci gaban mace a bude, hakan na iya sa cuta ya shigeta cikin sauki. Da wannan ne sai Allah yai mata wani ruwa na daban daga jikinta da zai rika wanke mata gabanta lokaci zuwa lokaci ba tare da sai tayi amfani da ruwa ko sai a lokacin da ta zo tsarki ba. Ganin cuta na iya shiga gaban mace a kowani lokaci, sai Allah Ya hukunta aikin wannan ruwan gaban mace a kowani lokaci cikin awanni 24.


Mata masu karancin shekaru sunfi ganin gabansu a jike a ko yaushe. Hakan na kasancewa ne saboda yadda jinin jikinsu yake da lafiya da kuruciya. Sannan kuma basu samun wadatar yin Jima'i kamar yadda mace mai aure take samu. Domin yawan Jima'i yakan rage fitowar wannan ruwan a gaban mace. Hakan nan idan mace shekarunta ya soma ja, ita ma ba kasafai za a rika ganin hakan daga gareta ba sai idan mace mai hali ce tana samun abincin da suke kara ni'ima sosai tana ci ko sha.


Masana sun hana mata amfani da foda ko turare a gabansu. Domin gaban mace bai bukatar wani ruwa ko sinadarin daga waje domin ya wanke shi. Wannan ruwan dai dake fitowa a jikinki shine ruwan dake kula da tsaftace gabanki da kuma yakar duk wata cuta da kan iya shiga farjin. 


Da fatan an ilimantu daga wannan bayanin, Allah ya datar damu amin. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post