Lafiya Jari: Illoli 4 da amfani 10 na tsamiya a jikin dan Adam -Android Pols



Tsamiya na daya daga cikin dangin ‘ya’yan itatuwan da al’ummar Hausawa musamman a Najeriya da kuma mutanen birnin Sin ke amfani da su sosai a rayuwar su ta yau da kullum.


Tsamiya ta na kunshe da sunadarai kamar haka: Magnesium, Potassium, Iron, Calcium, Phosphorus, Vitamin B1 (thiamin), Vitamin B2 (riboflavin), Vitamin B3 (niacin), vitamin C, vitamin K, vitamin B6 (pyridoxine), folate, vitamin B5 (pantothenic acid), copper da kuma selenium.


Tsamiya tana da tasiri masu tarin yawa ta fuskar inganta lafiya, haka kuma tana da wasu illoli idan aka sha ta ba bisa ka’ida ba. Ana amfani da tsamiya wajen sarrafa abubuwan sha, wajen yin magani, da kuma a girke-girke a matsayin abun karin dandano.


Ga wasu jerin matsaloli da tsamiya ke magancewa a jikin bil Adama kamar haka:


1. Cushewar ciki da rashin yin bahaya


2. Mura da zazzabi


3. Ciwon ciki


4. Tashin zuciya ga masu ciki


5. Tsutsar ciki


6. Matsolin da suka shafi hanta da madaciya


7. Tana wanke dattin ciki da kuma cushewar hanji


8. Ana amfani da ganyenta wajen magance cutukkan daji (cancer)


9. Ana tafasa ruwanta ayi wanka dashi dan magance ciwon gabobin jiki.


10. Tana sanya cin abinci domin kuwa tana sanya saurin jin yunwa


Illolin amfani da tsamiya sun hadar da:


1. Tsamiya za ta iya haifar da illa ga masu ciwon sukari saboda tana rage adadin sukarin da ke cikin jini. Haka ma ga wadanda za a yi wa tiyata, ana so su dakatar da shan tsamiya akalla makonni biyu kafin a yi aikin tiyatar saboda wannan dalili.


2. Ga ramammu, yawan shan tsamiya na iya kara rama. Ga masu kiba kuwa za ta taimaka masu wajen rage kiba


3. Ba a son a sha tsamiya da magungunan Ibuprofen da Aspirin saboda ta na kara adadin su da ke shiga jini. Idan haka ya faru, magungunan ka iya yin yawa su haifar da matsala.


4. Shan tsamiya a kai a kai yana rage karfin sha'awar namiji.


Wannan sune wasu daga cikin amfanin da tsamiya ke yi ga lafiyar jikin dan adam da kuma illolinta. Da fatan za ku kula sosai a yayin da kuke yin amfani da tsamiya don kare lafiyar jiki. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post