Sahihin Maganin Gyambon Ciki (ULCER) Ga Masu Yin Azumi


Cutar Ulcer shine samuwar kurji ko gyambo acikin daya daga cikin bangarorin hanjin mutum. 


Sababin dake haifar da hakan kuwa shine kamar haka;


1 Damuwa irinta rayuwa.

Masana kiwon lafiya sun bayyana cewa shiga damuwa kan jawo mutum ya kamu da cutar gyambon ciki (ulcer). 


2 (Gastro intestine) wato yayin da sunadaran da suke diga a cikin hanji don narkewar abinci sukayi karanci, suna iya samarda Ulcer.


3 Amfani da tukwane ko kwanukan alminium wadanda ake wankesu da soson karfe, wato birbishin aluminium din dake makalewa a jikin kwanon, shima yana kawo ULCER. 


4 Wani likita yana cewa, abinda ake kankarewa a jikin recherge card (katin Waya) yana kawo Ulcer idan a ka ci abinci ba tare da an wanke hannu ba.


5 Yawan amfani da abinci ko abin sha mai tsananin sanyi ko zafi. Masu cin abinci mai tsananin zafi ko shan abu mai tsananin sanyi na iya haddasa musu ciwon ulcer. 


6 Rashin tsabtace abinci ko abinsha, domin akwai wasu kwayoyin halittu kanana wadanda suke iya rayuwa a jikin mutum kuma har su yi tasiri a hanjinsa.


Manzon ALLAH S.A.W yana cewa Tsabta tana cikin Imani!


Maganin Ulcer mafi shahara da tasiri da yaduwa acikin littattfan likitancin musulunci suka ambata shine.


Ana hada Zuma (Honey) da garin Habbatus Saudah (Negela Sativa) da garin bawon Rumman (Pomgrenate) sai a hadasu a guri guda arika shan cokali 2 sau 3 a kullum.


Idan Ulcer din ta kai  nau'i na karshe daga nau'ukan Ulcer wato (Papetic Ulcer) ana gane wannan nau'i ne yayinda aka yi gyatsa sai aji warin jini.


Idan Ulcer takai wannan mataki, sai akara garin yayan KUMASARI (Pear) awancan hadin da muka fada.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post