Har Tayin Naira Miliyan 100 Aka Yimin Domin Na Janye Daga Takara Inji Matashin Dan Majalisa


Sabon matashin dan majalisar jihar mai wakilatar karamar hukumar Nguru dake jihar yobe ya bayyana irin halin da ya shiga tun a lokacin da ya fito takara.


Lawan Musa Majakura wanda ya kayar da tsohon kuma shugaban majalisa Ahmad Mirwa Lawan da ya ya shafe sama da shekara 16 akan kujerar yace har tayin Miliyan 100 aka yi masa don ya bar takarar amma bai karba ba.


Da ake tattaunawa dashi Lawan ya shaidawa Jaridar Aminiya cewa wasu Jami'an gwamnati sun tukareni da miliyan 18 amma na nuna bana bukata daga baya suka kara ya zama Miliyan 100 amma duk da haka ban karba ba.


Na sanar da su cewa mutanen kauyenmu sune suka saya min form saboda suna tunanin cewa zan yi musu ayyukan alheri don haka babu wani darasin zai sa na bar wannan takarar da nake yi har kuma Allah yasa nai nasara. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post