Yan Hisbah Sun Cafke Wani Kasurgumin Boka Kan Laifin Yiwa Wata Mata Ciki - Android PolsHukumar Hisbah ta jihar Kano a arewacin Najeriya ta kama wani boka da ake zargi da yi wa wata mata ciki bayan ta je wajen sa neman magani.


Bokan mai suna Muhammad Mansur, mazaunin karamar hukumar Dawakin Kudu an kama shi bayan matar da ba a bayyana sunanta ba, ta kai kara tana neman a bi mata hakki dauke da cikin wata bakwai.


Rahotanni daga garin na nuna cewa bokan ya yi fice wajen yaudarar mata, ciki har da matan aure.


Bokan na yaudarar mata ta hanyar shaida masu cewa idan suka kwana da shi zai ba su maganin da zai hana a yi masu kishiya da kuma samun damar mallakar miji.


Ta faɗa wa Hisbah cewa lokacin da ta je neman maganin wajen bokan ya shaida mata cewa ba zai yiwu ba, sai sun kwana tare.


A cewar ta, mutumin ya jima yana neman saduwa da ita, idan sun je wajen tare da mahaifiyarta, amma bai yi nasara ba har sai lokacin da ta ziyarce shi ita kaɗai.


Bokan, Muhammad Mansur ya amsa wannan laifi, sai dai ya ce aikin shaiɗan ne.


Shugaban rundunar Hisbah reshen karamar hukumar, Ustaz Kabiru Musa Dawakiji, ya ce za su ci gaba da bincike domin ɗaukan mataki.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post