Mu 'Ya'yan Tinubu Da Ganduje Ne, Cewar Wasu Daga Cikin Jaruman Kannywood - Android Pols


Fitacciyar furodusa kuma jaruma, Mansurah Isah, ta bayyana cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano shi ne ya ɗauki ‘yan fim na Kannywood ya miƙa su ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, shi ya sa ake ganin kusan dukkansu su na tafiyar jam’iyyar ne.


Masu lura da harkokin masana’antar finafinan sun ga yadda ‘yan fim su ka yi dumu-dumu a cikin harkar siyasa a wannan lokacin, amma a maimakon yadda su ke raba ƙafa a baya sai su ka bayar da ƙarfin su a ɓangare guda. 


Kusan kowane jarumi ko mawaƙi da ya shahara da wuya ka ji ba ya tafiyar jam’iyyar APC, kuma wasu jaruman da a da ba sa shiga harkar siyasa sai a bayan fage, yanzu sun fito tare da su ake tafiya tallar Tinubu.


A ganin wasu masu lura da al’amuran Kannywood, bin ɗan takara ɗaya tilo kamar ragon azanci ne.


Da mujallar Fim ta tambayi Mansurah Isah nata dalilin na yin dumu-dumu cikin harkar siyasa tare da dunƙulewar su ‘yan fim a waje guda, sai ta ce: “To da man ni ina siyasa ana ba ni aikin talla da kuma wasu ayyuka, amma dai ban taɓa shiga harkar na yi yawo ina bikin ɗan takara ba sai a wannan lokacin.


“Kuma ba ni kaɗai ba, mu na da yawa mata da Maza na cikin Kannywood.


“Amma dai a yanzu mun lura da halin da ake ciki, don haka mu ka fito mu nemi ‘yancin mu ta hanyar shiga siyasa da kuma zaɓar ɗan takarar da zai kawo mana cigaba da zaman lafiya a ƙasar mu.”


A kan dalilin su na bin Tinubu, Mansurah ta ce, “A nan Kano kowa ya sani mu ‘yan fim ‘ya’yan Baba Ganduje ne kuma da yake ɗan takarar shugaban ƙasa na APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mutum ne da ya ke son ‘yan fim, to da ya zo Kano sai Baba Ganduje ya ce, ‘Ga ‘ya’ya na, na ba ka su ka yi tafiya da su don za su yi amfani a yaƙin neman zaɓe.’ Kuma alhamdu lillah an ɗauke mu a matsayin ‘ya’ya duk inda za a je ko a jirgi ko a mota da mu ake zuwa.


“Don haka duk wani dan fim a Kano ɗan Baba Ganduje ne, don shi baban mu ne kuma masoyin mu ne. Tsakanin mu da shi sai godiya.”

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post