Innalillahi! Yadda motar su daraktan Kannywood Aminu S Bono ta kone kurmus a garin JosMotar su Darakta a masana'antar Kannywood Aminu S Bono ta kone kurmus a hanyar su ta zuwa biki garin Jos dake jihar Filato. 


Lamarin dai ya faru ne a ranar juma'a, 9 ga watan Disamba 2022, kamar yadda shafin film magazine ya rawaito. 


Sai dai kamar yadda yai karin bayani yace babu wanda lamarin ya rutsa dashi, domin lokacin da abin ya faru sun dawo daga wajen dinner motar tana ajiye abin ya faru. 


Muna Shirin tafiya wajen buga wasan kwallon kafa duk a cikin shagalin bikin kawai sai motar ta kama da wuta kuma nan take ta kone kurmus. 


S Bono ya bayyana takaicinsa da konewar motar duk da ba'a yi asarar rai ba amma yayi asarar Muhimman abubuwan sa na amfani da suke a cikin motar wanda suka hada da takardun makaranta da sauran muhiman takardu. 


Tun bayan faruwar lamarin jama'a da dama ne  musamman a Kannywood ke ta turawa da sakon jajantawa ga darkata S Bono. 


Muma anan muna roƙon Allah SWA ya tsayar a nan. Mu na fatan Allah ya saka maka da mafificin alkhairi. Allah ya mayar maka da sabon arziki, don darajar mafificin Halitta, Annabi  (SAW). 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post