Cike tallafin Naira dubu 30 da aka Yaudari mutane cewa daga Tinubu ne ashe na bogi ne


A sakamakon cike wani link da mutane suka dinga yi wanda ake cewa na tallafin dubu 30 ne da Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC Ahmad Bola Tinubu  zai bayar. 


Hakan yasa mutanen da suka shiga link din suna cikewa domin samun tallafin. Sai dai ashe ba na gaskiya bane na bogi ne wasu suka kirkira domin su debewa mutane kudaden su daga asusunsu na banki. 


Wadanda suka cike tallafin sun karbi sakonnin cire musu kudade daga cikin asusunsu, wanda hakan yasa suka dinga zuwa bankin da suke ajiyar kudaden su. Yawanci wanda suke ajiya a bankin GT, da kuma Zenith bank. 


A halin yanzu haka, rashin jituwa ya afku a tsakanin masu tu'ammali da waɗannan bankunan guda biyu na GT da ”Zenith” duba ga yadda aketa yi musu zari ɗai-ɗai na makudan kuɗaɗen su dake cikin asusun bankinsu kai tsaye ba shamaki. 


Sai dai bankunan suna hakurkurtar da mutanen da lamarin ya shafa inda suke cewa za su yi kokarin ganin an dawo musu da kudaden su. 


Sannan kuma sun gargadi sauran mutane da su daina bude dukkan wani link da aka turo musu a matsayin bayar da tallafi har sai an tabbatar da sahihancinsa don gujewa daga masu damfara. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post