Yadda Kiristoci Suka Karrama Wani Matashi Da Ya Haddace Al-Qur'ani A Kaduna


Malaman Addinin Kirista a Jihar Kaduna sun karrama wani yaro da ya haddace Al-qur'ani maigirma Jim kadan bayan yin makon ranakun fahimtar mabanbanta addinai da kabilu a fadin duniya wanda aka ware ranakun 13 ga Nuwamba har zuwa 16. 


A cikin wadannan ranaku na makon fahimtar juna, manyan malaman addinin Kirista sun kai ziyarar karrama Abubakar Ibrahim, wani matashin da ya rubuta Al-qur'ani da ka.


Shafin Muryar Amurka, ya rawaito cewa, Pastor Yohanna Buru shine ya jagoranci malaman addinin Kiristan zuwa wannan tsangaya. Ya kuma bayyana cewa, girmama matasan da su ka yi bajinta zai taimaka wajen jawo hankalin sauran matasa don gujewa ayyukan masha'a. Ya ce wannan mako na fahimtar juna zai kara dunkule kan al'umma don kawo cigaban kasa.


A nashi bayanin, Alaramma Ibrahim mahaifin matashi Abubakar Ibrahim wanda ya rubuta Al-qur'ani da ka ya ce ziyarar malaman Kiristan za ta kara karfafa zumunci tsakanin Kirista da Musulmi. 


Shafin na Muryar Amurka ya tattauna da Matashin inda ya yi bayanin yadda ya samu wannan baiwa ta rubuta Al-qur'ani ba tare da dubawa ba. Ya ce tun yana yaro ya fara nuna shi'awar rubuta Al-qur'ani kuma mahaifin shi ne ya kara karfafa shi.


Jahar Kaduna na cikin jihohin Najeriya da ke da kabilu da mabiya addinai daban-daban wanda kuma a baya an sha samun rikicin kabilanci da addini a jahar saboda rashin fahimtar juna.


Sai dai irin wannan ranaku da majalissar Dinkin Duniya ta ware na samun fahimtar juna a tsakanin mabiya addinai da kabliu zai kawo sauyi na samun rigingimun kabilanci da addini a kasar baki daya. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post