Gaskiyar Lamari Akan Labarin Ummi Rahab Na Samun Juna Biyu


A satin da ya gabata ne dai wani labari yai ta yawo a kafafen sada zumunta na zamani inda aka dinga bayyana cewa Ummi Rahab matar Lilin Baba ta samu juna biyu. 


Sai dai kuma wani bincike ya gano cewa ba jarumar ce ta wallafa wannan labarin ba, domin dama sanarwar ta fito ne da Shafin Instagram mai suna "Matar Lilin Baba Official". 


Inda aka wallafa cewa “I’m pregnant”, Wanda hakan yasa mutane suka dinga tunanin cewa tsohon Shafin jarumar ne, inda aka dauki labarin aka yayata shi a duniya. 


Wanda bayan fitar labarin a gidajen jaridu daga bisani wanda suke da alaka da Ummi Rahab suka fito suka dinga bayyana cewa labarin karya ne kuma ba jarumar ce ta wallafa ba, wasu ne suka yi amfani da sunanta suka wallafa labarin karya. 


Sai dai kuma jin wannan maganganu sun yi yawa yasa shafin "Mujallar Film" ya tuntubi wani makusanci ga mijin Ummi Rahab inda ya karyata labarin. Kuma Shima Lilin Baba ya tabbatar da cewa karya ne. 


Wanda a ranar juma'a Ummi Rahab da Lilin Baba suka nuna rashin jindadin su akan fitar da wannan labarin na karya. 


Daga bisani an gano cewa wani matashin mawaki ne mai neman suna ya kirki Shafin na bogi da sunan "Matar Lilin Baba Official" inda yake dauko hotunan ta da bidiyon ta daga ainihin shafinta yana dorawa da nufin itace. 


Matashin dai akwai kyakyawar alaka tsakaninsa da Ummi Rahab kafin ta yi aure, wanda a lokacin wasu suka dinga tunanin ko soyayya suke yi. 


Yawancin dai jaruman Kannywood suna fuskantar irin wannan matsalolin inda wasu ke yin amfani da sunan su suna bude shafuka a soshiyal midiya a matsayin sune

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post