Wani Fasto Ya Yaudari Mabiyansa 'Yan Gida Daya Ya Yi Musu Fyade


Ana zargin wani fasto da yi wa wasu kananan yara ’yan uwan juna fyade har daya daga cikinsu ta samu juna biyu. Yarinyar da wannan fasto ya yi wa ciki tare da ’yar uwarta mabiyansa ne a wani cocin Cherubim And Ceraphim da ke a Jihar Ogun.


Abimbola Oyeyemi wanda shine Kakakin ’yan sandan jihar, ya ce, “kananan yaran sun bayyana cewa idan suka je yin addu’ar dare a cocin, faston kan kai su gidansa, ya tursasa su tsoti wani wanda ke sa su barci nan take, idan sun farka za su ga an yi amfani da su.


“Da aka tambaye su abin da ya hana su fada wa kowa, sun ce faston ya yi barazanar kashe su idan suka kuskura suka gaya wa wani.”


Oyeyemi, ya ce faston, mai shekara 30, ya shiga hannun, bayan mahaifin yaran ya kai kara Ofishin ’yan sanda.


Ya ce mahaifin kananan yaran ya kai kara ne bayan ya gano cewa babbar mai shekara 16 tana dauke da juna biyu.


Ya bayyana cewa limamin cocin ya amsa zargin da ake masa a lokacin da ’yan sanda ke yi masa tambayoyi.


Ya kara da cewa Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Ogun, Lanre Bankole, ya sa a gudanar da cikakken bincike kan lamarin sannan a gurfanar da malamin addinin a kotu.


A baya-bayannan dai ana yawan samun fastoci da zargin cin zarafin mabiyansu. Sai dai wasu na bayyana hakan da cewa ba fastoci gaskiya bane domin cikakken fasto ba zai aikata hakan ba. 


Yayin da wasu kuwa ke cewa rashin daukar mataki ne yake jawo wasu fastocin ke cigaba da yin amfani da matsayinsu suna cin zarafin mabiyansu. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post