Kaunar Da Nake Yiwa Matata Yasa Na Karbi Addinin Musulunci


Wani dan Najeriya mai suna Ossai ya musulunta domin ya auri matarsa saboda soyayyar da yake yi mata. 


Wani shafin Hausa na Instagram, Arewa Fashion and Style ne ya watsa labarin a ranar Litinin, 21 ga Nuwamba, 2022.


Sabuwar amaryar, wacce ta amsa wallafa wani rubutu na taya murna a karkashin sakon, ta ce da farko mahaifinta ya nuna shakku game da musuluntar mijinta. 


"Na je ganin mahaifina na gaya masa game da hakan, da farko bai ji daɗi ba domin ya kasance yana shakku game da musuluntar masoyin nawa kuma yana tsoron ko zai koma addininsa na da idan ya samu abinda yake so.


Daga karshe dai Babana ya amince har aka sanar da watan Oktoba don fara shirye-shiryen auren, amma a sakamakon rasuwar mahaifiyarsa yasa ba'a yi bikin a watan Oktoba ba hakan yasa aka dage bikin har zuwa watan Nuwamba amma yanzu anyi auren Alhamdulillahi tace. 


A wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram, May Haidar, daga jihar Kaduna, ta rubuta; 


"Alhamdulillah na samu labarin abubuwan rayuwata da nake yi muku ERKEGIM, ina mai yiwa Allah godiya da yasa muka dauki tsawon lokaci muna soyayya cikin dadi da akasin hakan. Ina fatan rayuwar da za mu yi nan gaba ba za ta kasance mai kunci ba.... Na gode da kuke nuna kaunar ku gareni ni da mijina. 


Ossai ya kuma wallafa hotunan bikin aurensu a ranar 17 ga Nuwamba, 2022 kuma ya bayyana matarsa May_Haidar a matsayin abar kaunar su. 


"Ni da matata Ina taya mu murna mara iyaka. Domin ni da ita mun zama tamkar jini da tsoka Ita ce Kashin jikina da nama.  

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post