Ana Zargin Jaruma Amal Umar Da Saurayinta Kan Damfarar Wasu Makudan Kudade


Fitacciyar jarumar Kannywood Amal Umar na cikin tsaka mai wuya inda ta nemi kotu da ta dakatar da mataimakin sufeton 'yan sanda mai Kula da shiyya ta daya da kwamishinan 'yan sandan Kano da wani jami'in Dan sanda mai bincike Kada su kamata.


Shafin Freddom Radio ya rawaito cewa ana zargin saurayin jaruma Amal mai suna Ramadan Kan zargin yin damfara wasu makudan kudade wanda Kuma bayan an Kama shi ya tabbatar da cewa ya kashewa budurwarsa Amal kudin.


Tun da farko dai wani mutum ne ya Kai karar saurayin Amal ga 'yan sanda cewa ya bashi kudi har Naira Miliyan 40 domin yin kasuwancin wayoyi amma ya neme shi ya rasa, wanda hakan yasa 'yan sanda suka kamo Ramadan din.


Sai dai bayan bincike da Hukumar 'yan sanda ta gudanar saurayin ya tabbatar da cewa ya siyawa budurwarsa Amal Mota, Kuma ya bata Naira Miliyan biyar ta bude shagon sayar da kayayyaki.


Hakan yasa 'yan sanda suka kama Amal inda suka fara bincike akanta tare da kwace motar, wanda hakan yasa jarumar ta garzaya Kotun jiha mai lamba 17 dake Miller road a Kano inda ta nemi Kotun da ta dakatar da 'yan sanda daga yukurin da suke yi na kamata.


Yanzu dai Kotun ta saka ranar 16 ga watan Disamba domin sake zaman shariar, kamar yadda Shafin Freddom Radio ya rawaito. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post