'Yar Najeriya Ta Mutu A Yayin Da Likitoci Ke Yimata Tiyata Don Kara Mata Girman Mazaunai (hipps)


Labarin wata tsaleliyar budurwa 'yar asalin Najeriya Amelia Pounds 'yar shekara 28 yaja hankalin al'umma a fadin duniya wacce ta rasa ranta yayin da ake yi mata tiyata don Kara mata mazaunai. 


Matashiyar taje kasar India ne domin yi mata aikin gyaran jiki da kara mata girman mazaunai a wani asbiti dake New Delhi a ranar Juma'a. Sai dai ba'a samu nasarar yin aikin ba inda ana tsaka da yi mata ta rasa ranta. 


Vera Sidika wani mai yin amfani da shafin Twitter shine ya wallafa labarin inda ya tabbatar da mutuwar Matashiyar. Shima shafin watsa labarai na LindaIkeji ya wallafa labarin a ranar Asabar. 


Wannan dai ba sabon abu bane na yadda ake samun asarar rai a yayin gyara ko canja hallita da wasu mutane cikin maza suke zuwa wajen likitoci suna yi musu. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post