'Yan bindiga sun kai hari a babban asibitin Naija sun yanka ma'aikaci da yin garkuwa da ma'aikata da dama



Wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne sun kai hari kauyen Gulu da ke karamar hukumar Lapai a jihar Neja da misalin karfe biyu na safiyar ranar Talata. 


An tattaro cewa ‘yan ta’addan sun kai harin ne a babban asibitin Abdulsalam Abubakar inda suka yi wa wani mutum da ke yin aiki a asibitin yankan rago. 


'Yan ta'addan sun kuma yi garkuwa da mutane a kalla 10 a harin da suka kai da safiyar Talata. Daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su har da wani likita mai suna Ben, da kuma wani mai harhada magunguna da ke aiki a asibitin.


Wata majiya daga Abu Qudama da ta bayyanawa SaharaReporters yadda lamarin ya faru, inda yace mazauna garin Gulu da dama sun fara Kauracewa yankinsu zuwa yankunan da ke kusa saboda fargabar sake kai wani hari. 


Ya ci gaba da cewa, “Na farka ne da wani kira da aka yi da safiyar yau, cewa ‘yan bindiga sun kai wa al’ummar Gulu da ke karkashin karamar hukumar Lapai ta Jihar Neja hari, kuma a yayin kai harin ne aka yiwa wani ma’aikacin babban asibitin Gulu yankan rago tare da yin garkuwa da wasu da dama da ‘yan fashin suka yi. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. 


“Yaya mutane za su zama marasa Imani a duniya har za a yanka mutum kamar dabba? Wannan shi ne daya daga cikin labarai masu ban tsoro da raɗaɗi da suka ci karo da ni a wannan watan.


“Duk da haka, a wani yunkuri na neman tsira, tun daga lokacin mutanen Gulu ke yin hijira zuwa kauyukan da ke makwabtaka da birnin Lapai. A kan wannan batu, ina kira ga jami'an gwamnati da hukumomin tsaro da su dauki kwakkwaran mataki na dakile wannan tsattsauran ra'ayi don gujewa kutsawa gaba.


“Don haka ina addu’ar Allah ya sa duk wanda ya rasa ransa a kan wannan aiki ya samu zaman lafiya a kabarinsa. Ameen. Allah ya dawo mana da zaman lafiya a jiharmu da al'ummarmu da Najeriya baki daya." 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post