Kotu na neman Hannatu Bashir kan karar da Ali Nuhu ya shigar da yake zarginta da bata masa suna


Babbar kotun majisatare dake noman salad ta bayar da umarnin a gurfanar mata da Hannatu Bashir a gaban ta kan korafin da Ali Nuhu ya shigar. 


Tun da farko dai Ali Nuhu ne ya shigar da Kara a kotun kan zargin jaruma Hannatu Bashir da ci masa mutunci da bata masa suna. 


A ranar Litinin ne kotun ta zauna inda ta saurari Karar daga wajen Lauyan mai karar wanda bayan hakan Lauyan mai karar da kuma Lauyan wacce ake zargi da yin laifin sun bayyanawa kotu cewa za suje su sasanta kansu. 


Sai dai kotun ba ta amince da hakan ba inda ta bayar da umarnin cewa dole ne sai wacce aka kawo Kara ta bayyana a gaban kotun. Inda ta saka ranar 25 ga watan Oktoba a matsayin ranar da za'a cigaba da zaman shariar. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post