Rahotannin dake ci gaba da yawo a kafafen sada zumunta na tabbatar da cewa an wata sa-insa da ta kaure a tsakanin jaruman biyu Ali Nuhu da kuma Hannatu Bashir.
Tun da farko dai Ali Nuhu ne ya kai ƙarar Hannatu Bashir zuwa kotu kan zarginta da famadasa bakaken maganganu ta hanyar sakon tes.
Mujallar Film ta wallafa labarin a shafinta na facebook inda tace lauyar Ali Nuhu Salima Muhammad itace ta shigar da ƙara a babbar kotun Majisatare dake NomanSalad a birnin Kano.
Mujallar Film ta bayyana dalilin da ya jawo sabani a tsakanin jaruman wanda ita Hannatu ta gayyaci Ali Nuhu wani sabon Film da take shirin yi wanda kuma Ali Nuhu zai fito a ciki, sai dai kuma an bashi kudi amma duka da haka sai da ya saɓa bai je wajen daukar Film din ba.
Ranar 10/10/2022 aka yi alƙawari da Ali Nuhu domin zuwa wajen aikin daukar Film din amma kuma sai Ali Nuhu bai halarci wajen ba inda aka bayyana cewa baya gari. Wanda rashin zuwan nasa yasa aka tilasta fasa aikin film din.
Hakan yasa aka ɗage har zuwa rana mai zuwa,sai dai duk da hakan Ali Nuhu bai samu zuwa ba, wanda aka ƙara cewa ai bai dawo saga tafiyar da yai ba a ranar ake sa ran zai dawo kuma ko ya dawo ba zai samu zuwa a wannan ranar ba.
Lamarin da ya dugunzuma jaruma Hannatu inda ta tura masa sakon kar ta kwana tare da fadama Ali Nuhu cewa ba ta son aikin nasa. Wanda shima daga bisani ya mayar mata da martani mai zafi har yai ikirarin makata a kotu.
Daga bisani bayan an tuntube Ali Nuhu kan lamarin sai Jarumin ya ce ko kaɗan shi bai rattaba wata yarjejeniya da Hannatu ba cewa zai yi mata fim ba, kuma shi bai da wata hulɗar kasuwanci da ita da har za ta tura masa tes ta gaya masa baƙar magana wadda ɓatanci ne a gare shi tare da zubar masa da ƙima a idon jama’a.
Don haka ne ya kaita kara a gaban kotu domin ta ɗauki matakin shari’a na ɓata masa suna da cimasa mutunci da Hannatu Bashir taimasa. Ya ɗauki hoton sakon da ta turamasa ya haɗa da takardar ƙara ya mika ga kotu.