Rikici ya barke tsakanin Rahma Sadau da Mansura Isah tun bayan fitar da jerin sunayen jaruman Kannywood da Nollywood su 33 da za su yi wa Bola Ahmad Tinubu kamfen a zaɓen 2023. .
Rahama Sadau na ɗaya daga cikin jerin jaruman da aka fitar da sunanta, wanda daga bisani ta fito ta ƙaryata hakan, inda ta nesanta kanta daga cikin wanda za su yi kamfen ɗin a wani rubutu da ta wallafa a shafinta na twitter inda ta bayyana hakan da babbar ƙarya.
Sai dai daga bisani Mansura Isah ta mayar mata da martani inda ta ce dama tun farko ba sunanta aka yi niyyar sakawa ba kuskuren rubutu ne. Wanda hakan ya kara fusata Rahama Sadau inda ta ƙara mayarwa da Mansura Isah martani mai zafi.
A martanin da Rahama ta mayarwa da Mansura Isah ta fadamata cewa iyayen gidanta sun kirawo ta sun bata hakuri akan kuskuren da aka yi na saka sunanta a masu yiwa Tunubu Kamfen.
Ta kara jan kunnen Mansurah cewa, "Zuwa ga Mansura Isa, ina ba ki shawarar ki bar abin nan ya wuce saboda magabatan ki sun kira ni ‘a cikin sirri’ don neman afuwa kan ‘kuskuren da aka yi da gangan’. Ba sai kin ari bakin wani kin ci masa albasa ba. Sai anjima.”
Sai dai wasu na ganin abinda Rahama ta yi bai dace ba domin wannan bai kai abinda za'a tsaya ana cacar baki ba.