Rahama Sadau Ta Nesanta Kanta Da Kamfen Din Bola Ahmad Tinubu


Rahama Sadau ta nesanta kanta daga cikin sunayen da aka fitar na jaruman Kannywood da za su yi kamfen ga ɗan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC Bola Ahmad Tinubu a zaben 2023.


Legit Hausa ta rawaito cewa A cikin jerin sunayen jaruman Kannywood da Kuma Nollywood su 33 da za su yiwa Bola Ahmad Tunubu Kamfen akwai manyan jarumai wanda taurarawarsu ke haskakawa a masana'antar film.


Cikin sunayen ƴan Kannywood har da Rahama Sadau wacce ta nesanta kanta daga cikin wanda aka fitar da za su yiwa Tunubu Kamfen. "Inda ta bayyana cewa wannan karya ce kuma mara tushe domin ita ba ta cikin mutanen da aka ambata".


Rahama Sadau ta bayyana hakan ne a shafinta na twitter inda tace ita ba ta san wannan batun ba domin karya ce kawai, kuma ba ta da wata alaƙa da wannan kamfen din.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post