Jarumin Barkwanci Baba Ari Ya Yiwa Malamar Islamiyya Dukan Tsiya Saboda Ta Hukunta 'Yarsa



Ana zargin fitaccen jarumin barkwanci a masana'antar Kannywood Ari Baba ya yiwa wata Malamar makarantar Islamiyya dukan tsiya saboda ta hukunta 'yarsa Hafsat kan wani laifi da ta yi. 


Safiya Nasir wacce itace Malamar su Hafsat ta bayyana cewa tana aji tana biya musu karatu sai ta hangi Hafsat ita da kawarta suna cin cingam wanda hakan yasa aka yi musu magna domin su daina amma ba su daina ba hakan yasa na dauki bulala na dake su. 


Sai dai ita Hafsat ta nuna cewa ba za a dake ta ba wanda bayan fara dukanta sai ta zube a kasa da nufin ta tayar da Aljanu wanda kuma karya take yi. 


Wanda hakan yasa daga baya ta je ta sanar da mahaifinta cewa an yi mata dukan kawo wuka an tayar mata da Aljanu, hakan yasa Mahaifin nata ya taso ta a gaba suka zo makaranta inda yake tambayar Hafsat ta nuna masa wanda ya dake ta. 


Ana nuna masa ni kawai sai ya jawo hijabi na ya kifa min mari wanda na gigice na tube a kasa. Inda ya fara takani da takalmi yana bugun bayana. 


Sai dai daga bisani a wata hira da gidan Radio Freedom suka yi da Ari Baba ya nuna nadamarsa akan matakin da ya dauka inda ya ce shi wallahi kawai dankwalin ta ya ja. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post