Dalilin da yasa Ali Nuhu ya janye karar da yakai Hanan gaban kotu


Jarumi Ali Nuhu ya janye karar da yakai jaruma Hannatu Bashir kotu bayan kalubalantar ta da cin zarafinsa da ta yi a wani sako ta kafar sadarwa ta zamani. 


Tun da farko dai Hannatu Bashir da ake Kira da Hanan ta tuhumi Ali Nuhu da bata mata lokaci da yai Kan wani aiki da zai yi mata a wani sabon film da take shiryawa. 


Sai dai Ali Nuhu bai halarci wajen daukar film din ba har Karo biyu wanda ya bayyana cewa ya yi tafiya baya gari. Hakan yasa ita jarumar ta tafka babbar asara. Wanda daga bisani ta turamsa da sako cewa ta hakura da aikin nasa. 


Wanda kalaman suka yiwa Ali Nuhu zafi shi Kuma ya dauki matakin shigar da ita gaban kotu. Sai dai a zaman Kotun na farko da ya gudana jarumar ba ta halarta ba hakan yasa Kotun tai umarni da jarumar ta bayyana a zama na gaba. 


Sai dai a zaman Kotun da ya gabata a ranar Alhamis jaruma Hannatu ta halarta. Sai dai lauyan Ali Nuhu ya bayyanawa alkali cewa wanda ya shigar da karar ya janye domin sulhu suke yi a tsakanin su. 


Sai dai alkali ya tuhumi jaruma Hannatu da rashin halartar zaman Kotun na farko inda ta bayyana cewa a lokacin ba ta da lafiya, hakan yasa Kotun ta yi mata afuwa. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post