Yarinya 'Yar Shekara 13 Ta Haddace Alqur'ani Maigirma Tare Da Rubuta Shi Da Ka A Kastina


An samu wata matashiya yar shekara 13 a kauyen Kagara dake karamar hukumar Kafur ta jihar Katsina ta haddace Alqur'ani maigirma tare da rubuta shi da ka 


Bello Abdulkadir wanda shine Hakimin Mahuta ya bayyana farin cikinsa a lokacin wani taro da akai na karrama Matashiyar, inda yace suna farin ciki da wannan baiwa da Allah yaiwa matashiyar. Ya bayyana cewa wannan babbar nasara ce ga kauyen Mahuta da jihar katsina da duk wani musulmi dake fadin duniya. Abdulkadir ya kuma yabawa iyaye, malamai da sauran shugabannin al’umma kan yadda su ke kula da tarbiyyar ƴaƴansu yadda ya kamata, yana mai kira gare su da su ci gaba da yin hakan.


Danejin Katsina, ya baiwa sarakunan jihar tabbacin cigaba da bada goyon baya ga duk wani abu da ya shafi addinin musulunci, domin cigaban yankin baki ɗaya.


Shugaban karamar hukumar Kafur, Garba Kanya, ya yaba da kwazon yarinyar tare da bada tabbacin tallafa mata a matakin sakandire da manyan makarantu.


Shugaban makarantar ta, Madrasatul Tahfiz, Sheikh Sani Kagara, ya ce an kafa makarantar ne da nufin yin tasiri na ingantaccen ilimin addinin Musulunci a tsakanin matasa a cikin al’umma.


A cewarsa, yarinyar ta haddace Alkur’ani ne a cikin shekaru huɗu, kuma ya danganta nasarar da ta samu ga goyon bayan iyayenta da jajircewar malamanta a makaranta.


A nasa jawabin, mahaifin hafizar, Ahmed Sani, ya yaba da duk tallafin da aka ba shi da ƴarsa, inda ya yi kira ga iyaye da su bar ƴaƴansu su samu ilimin addinin musulunci da na boko.


Ya kuma ba da tabbacin ci gaba da ba ta goyon bayan da ya dace don kuma ta ci gaba da karatun ta na yamma, inda ya ce a halin yanzu tana makarantar firamare a yankin. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post