Yanzu-Yanzu Bankaura Wanda Aka Fi Sani Da Kafi Gwamna A Shirin Film Din Kwana Casa’in Ya Rasu


Yanzu muke samun rasuwar Malam Umar Yahaya Manunfashi rasuwa bayan fama danna rashin lafiya wanda ya shafe makonni a  wani asibiti sake Kano. 


Falalu Dorayi shine wanda ya sanar da hakan rasuwar jarumin a shafinsa na Facebook inda yai rubutu Kamar haka:


"INNALILLAHI WAINNA ILAIHI RAJI'UN! 

Allah yai maka rahma Baba Umar

(Bankaura/Kafi Gwamna)


Umar Yahaya Mununfashi na daya daga cikin Iyaye Jarumai da suke bada muhimmiyar gudunmawa a Masana’antar Kannywood. Tun daga Stage Drama zuwa Television har Home Video (Kannywood) Sannan Babban Ma’aikaci ne A Nigerian Customs Service.


Allah Yai masa gafara ya bawa iyaye da iyalai da Yan uwa hakurin rashinsa. Idan mutuwar tazo Allah kasa mu cika da imani.

Amin."

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post