Na Shiga Siyasa Ne Domin Kawo Sauyi Da Canja Akalar Siyasar Najeriya - Cewar Alan Waka


Fitaccen mawaki a kasar Hausa Alhaji Lada Abubakar Alan Waka yadda bayyana cewarsa ya shiga harkar siyasa ne domin canja alkibilar siyasar da ake yi ta rashin tsari a Najeriya. 


A wata tattaunawa da yai da gidan jaridar Mujallar Film, Ala ya bayyana cewa yadda ake gudanar da siyasa a Najeriya babu tsari kuma babu alkibla. Hakan yasa muka shigo domin kawo gyara da canja alkibilar siyasar. 


Ya Kara da cewa ya shahara a harkar wakokin ilimantarwa, fadakarwa da Wakokin Sarakuna. Kuma na dade Ina siyasa sai dai ba ta fito fili ba sai a wannan lokacin inda na fito neman takarar zama dan Majalisar Tarayya mai wakilcin karamar hukumar Nasarawa a Kano. 


Kuma jama'a ne sukaga na cancanta da na fito yin takarar, domin suna ganina a matsayin sananne kuma wanda zai rike amana da kawo cigaba tare dashi sauya alkibilar siyasar da aka dade ana yi ba tare da wani cigaba ba. 


Kusan dukkan wakokin da nake yi Ina yin su ne a matsayin sadaukarwa ba don samun kudi ba hakan yasa jama'a suka zabe ni kan na fito nai takara kuma suna da yakinin cewa ba zan sauya daga yadda nake ba. 


Idan munyi nasara za mu kawo sauye-sauye tare da magance matsalolin da suka dabaibaye harkar siyasa don kawo cigaba mai amfani. Don haka jama'a su san ma'anar wakilci da kuma aikinsa, ko iya wannan na yi na tsaya na wayar da kan mutane a kan haka zan iya cewa na ci riba. Don haka yunkurin da na yi na fitowa takara shi ma na ci riba da shi, saboda a yanzu matasa iri na sun yarda cewa kowa ma zai iya. 


Don haka aikin da ya ke gaban mu shi ne mu wayar da kan matasa a kan siyasar ‘yanci da kuma wayewa. Sannan ya yi kira ga matasa akan su san kansu da 'yancin kansu. Kada su yi amfani da damar su ta hanyar da ba ta dace ba don biyan bukatun wasu. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post