Dan China Da Ya Hallaka Ummita Ya Nemi Kotu Da Ta Bashi Damar Daukar Lauyan Da Zai Kare Shi A Kotu


Geng Quangrong dan asalin kasar China da ake zargin sa da kashe budurwarsa har gidansu mai suna Ummakulsum Buhari wacce ake kira da Ummita 'yar kimanin shekaru 23 dake zaune a unguwar Janbulo cikin birnin Kano. 


Ana zargin Geng da yin amfani da wuka ya caccakawa Ummita wanda hakan yai sanadin mutuwar ta nan take. Wanda daga bisani aka gurfanar dashi a gaban wata kotu dake Sabon Gari karƙashin alkali Hanif Sanusi Yusuf.


Jaridar Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, a yayin zaman kotun Alkalin ya zargi Geng mai kimanin shekaru 47 da laifin aikata kisan gilla wanda ya saba da sashen na 221 na kundin penal code. 


A ranar Alhamis ne aka sake zaman shari'ar inda wanda ake zargi ya nemi kotu kan ta bashi damar ya dauki Lauyoyin da za su kare shi a gaban kotu. 


Barista Musa Lawan babban lauyan jihar Kano ya ce, tabbas zaman shariar ba zai cigaba da gudana ba har sai wanda ake zargi ya samu lauyan da za su tsaya masa. Don haka muna kira da kotun da ta dage zaman shariar har zuwa lokacin da ya samu lauyoyi da za su tsaya masa. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post