Jami'an Hukumar Karota A Jihar Kano Sun Yi Nasarar Kame Tirela Makare Da Giya


Hukumar Karota ta Jihar Kano tayi nasarar cafke motar Tirelar ranar Alhamis a kan titin Bello Dandago da misalin karfe 2:30 na daren  Larabar da ta gabata, a lokacin da suke kokarin su na shiga cikin Sabon Garin Kano


Gidan Express Radio Nigeria sun rawaito cewa Jami'an Hukumar Karota ne suka sami nasarar cafke motar a lokacin da suka bukaci direban motar ya gabatar musu da takardar shaidar abinda ya dauko ta Way bill, inda ya bayyana musu cewa Kwali ya dauko 


Bayan da jami'an suka matsa bincike sai suka tabbatar da giya ce a ce cikin babbar motar kirar tirela. 


Shugaban Hukumar KAROTA Hon Baffa Babba Dan Agundi ya bayyana cewa Hukumar KAROTA ba za ta gajiya ba wajen kama duk wani nau'in kayan da ya ci karo da su wanda dokar jihar Kano bata amince a shigo da su ba


Ya kara da cewa za'a kara baza jami'an KAROTA musamman kan manyan titinan jihar nan domin ganin an dakile shigowar kayayyakin da dokar jihar Kano ta haramta. 


Ƙasa da mako guda Hukumar ta cafke manyan motocin Tirela maƙare da giya wadanda adadinta ya kai fiye da Kwalba dubu arba'in (K40)da kudinta ya haura naira miliyan arba'in  (N40m)


Da zarar an kammala bincike za a miƙa giyar ga Hukumar Hizba domin daukar mataki na gaba.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post