Gwamna Buni ya bayar da gudunmuwar gidaje 3 ga matan malamin da aka kashe a Yobe, Goni Aisami


Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe a ranar Laraba ya bayar da tallafin gidaje uku ga matan  marigayi Sheikh Goni Aisami, wani malamin addinin Musulunci da aka kashe kwanan nan a jihar.


Da yake mika takardun gidajen ga Sarkin Bade da ke Gashua, Abubakar Umar Suleiman, Mista Buni ya ce tallafin ya kasance cika alkawarin da ya dauka na tallafa wa iyalan marigayi Aisami.


Mista Buni wanda ya samu wakilcin Babagana Kyari, mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin addini, ya ce matan su uku kowacce an bata gida daya da za su rika kula da ‘ya’yansu.


Da yake mayar da martani, Mista Suleiman ya gode wa gwamnan bisa kauna da goyon baya ga iyalan fitaccen malamin.


Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa, a kwanakin baya Buni ya bayar da aikin yi na din din din ga ‘ya’yan marigayin guda biyu.


NAN ta tuna cewa an yi zargin wasu sojoji biyu ne suka harbe malamin da aka kashe dan asalin garin Gashua a ranar 19 ga watan Agusta a Jaji-Maji, karamar hukumar Karasuwa ta jihar.


A ranar 27 ga watan Agusta ne rundunar sojin Najeriya ta kori Lance Kofur John Gabriel da Lance Kofur Adamu Gideon, tare da mika su ga rundunar ‘yan sanda a jihar domin gurfanar da su gaban kuliya.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post