Tsohuwar Jarumar Kannywood Maryam Mushaqqa Ta Aurar Da Santaleliyar 'Yarta
A ranar Asabar ne aka daura auren diyar jaruma Maryann Aliyu wacce aka fi sani da Maryann Mushaqqa. An daura aure ne a ranar Asabar 27 ga Augusta, 2022. 


Tsohuwar jarumar, wadda aka fi sani da Maryam Mushaqqa, ta auri Alhaji Muhamed Auwal Galadima ne a kasar Kamaru kimanin shekara 19, kuma auren ya yi albarkar ‘ya’ya da cigaban rayuwa.


Auren nasu babban misali ne na ‘yan fim masu yin aure su zauna, kuma ya karya lagon ikirarin da wasu ke yi cewar wai ‘yan fim mata ba su zaman aure.


A tattaunawar da su ka yi da mujallar Fim a ranar Lahadi, Hajiya Maryam da Alhaji Auwal sun bayyana matukar murna kan wannan abin farin ciki da ya same su na aurar da babbar ‘yar su.


Iyayen amaryar sun kuma yi tsokaci dangane da masu cewa ‘yan fim mata ba su zaman aure.


Mushaqqa ta ce: “Assalamu alaikum. Barkan mu da safiya, ina gaishe da kowa. Ina yi wa makaranta Fim Magazine fatan alkhairi. 


“Gaskiya ba zan iya misalta farin cikin da na ke ciki ba kasancewar ban saba ba, ban taba zaton zan yi tsawon rai har in ga wannan rana ba. So, ina cikin annashuwa da farin ciki, ina kuma addu’ar Allah ya ba su zaman lafiya, Allah ya kade masu fitina. Irin ni ma na yi suriki, ka gane irin abin! Abin na da dadi sosai, kuma abin alfahari ne.


“Allah ya sa mutu-ka-raba. Allah ya sa su yi dogon zango na rayuwa mai albarka, amin.


Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post