Tsantsar Soyayyar Rahama Sadau Ce Ta Sanyani Shiga Harkar Film - Naufal. S. Muhd


Amman abin haushin a hirata ta farko da (nasara radio)dake cikin garin kano na aibata babbar masoyiyar tawa, wacce na kwashi tsawon shekaru sama da goma ina dakon soyayyarta a cikin zuciyata


Sunana naufal. S. Muhd da aka fi sani da (realnaufal). Ni haifaffen garin kaduna ne, dan asalin garin Katsina, amman tsananin soyayyar Rahama Sadau ya ingiza rayuwata na koma garin kano da zama gami da  tsintar kaina a harkar film dumu-dumu har na tsawon shekaru biyu.


Ina taka rawa a bangaren jarumi, marubuci, da kuma mai bayar da umarni a cikin masana'antar film ta kannywood.


Na fuskanci kalubale kala-kala kafin na tsinci kaina a wannan matsayi, na jure na jajirce duk domin ceto soyayata akan abar kunata, tare da fatan wata rana Allah zai hadamu a wani aikin.


Amman abin takaicin anan shine na tsayin wannan lokacin Allah bai taba hadani da masoyiyar tawa ba. Ina cikin zaman jiranne aka gayyaceni hira domin a tattauna dani akan lamarin da ya danganci sana'ata ta film a nasara FM dake cikin garin Kano. 


A inda a cikin tattaunawar tamu ne akayi min wata tambaya dangane da matakin da ya kamata a dinga dauka akan Matan kannywood dake shigar banza a bayan fage. Ba tare da na yi dogon nazari ba, na kuma duba girman soyayyar da na ke yiwa babbar masoyiyar tawa ba, na bayar da shawara akan korace kawai tafi cancanta dasu, sannan na kawo misali da Rahama. 


Tabbas nayi takaicin wannan amsa da na bayar nayi danasanin wannan tattaunawa duk da kasancewarta tattaunawata ta farko da aka gayyaceni a gidan radio a matsayina na jarumi kuma mai bayar da umarni mai tasowa a kannywood. Nayi kuka kamar raina zai fita bayan kammala tattaunawar. 


A karshe Rahama inaso ki sani cewar ba nayi hakan bane da niyyar cin fuska ko nuna kiyayyata a gareki ba, hasalima ni babban masoyine boyayye a gareki mai dakon soyayyarki da tsananin kaunarki na tsawon shekaru sama da goma.


Da fatan idan kinyi katari da wannan hira ba za ki min mummunar fahimta ba, za ki min uziri, domin wallahi ina matukar sonki ina kaunarki ina bibiyar duk wani motsi naki a social media kuma ina supporting dinki duk rintsi duk wahala. 


A fagen mata masu matsayi a zuciyata daga mahaifiyata sai ke rahama ina neman afuwarki please. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post