Budurwa Da Aka Yi Garkuwa Da Ita A Jirgin Kasa Abuja - Kaduna Za Ta Angwance Da Dan BindigaA wata Majiya Dake Shaida Mana cewa, Shugaban masu garkuwa da mutane (Kwamanda) ya kyasa a yayin da yayi tozali da wata Shantaleliyar budurwan Mai Suna Azurfa Lois John Bayan tana daya daga cikin fasinjojin Jirgin kasa da su ka yi garkuwa da su daga Abuja Zuwa Kaduna cikin wasu watanni baya a watan Maris Wanda yayi daidai da 28.


Budurwar dai dalibace a Jami'ar Jihar Kaduna, inda take matakin aji uku, wacce aka yi yunkurin biyan diyyatarta, inda Kwamandan masu garkuwa da mutanen ya Shaida cewa shi fa yana son Mista John Kuma da aure, don haka da Kudin fansar iyayenta sune suyi shagalin biki.


A dai halin yanzu Kungiyar Kiristoci na Kasa wato CAN ta buga teburi, inda ta ce ba yadda za'ayi Mista Lois John ta Auri Dan Ta'adda.


Daga Barrista Nuraddeen Isma'eel. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post