Ni ba Jahila Bace Na Haddace Al-qur'ani Tun Daga Baqara Har Zuwa Nasi__Inji Safara'u


"Ni Ba Jahila bace na Haddace Al-qur'ani Maigirman tun daga Fatiha har Nasi, babu inda za'a ja mani ban ida kaiwa ba" 


Kamar yadda matashiyar mawakiyar da ke tashe wato, Kuma Jaruma a shiri Mai dogon Zango na Kwana Casa'in Safara'u ta Wallafa a shafinta na dandalin facebook, ta bayyana wasu muhimman zantuttuka dangane da kasuwancin da ta ke yi na rawa da waka kamar haka:


"Ni mahardaciyar Alƙur'ani Izif i60 ce, tun daga baƙara har zuwa nasi babu inda za kuyi min jaa ban kama na wuce ba Alƙur'ani Izif 60 ne cif cif a kai na".


"Don kun ga ina sana'ar rawa da waƙa hakan baya nuna cewa ni jahila ce ko kuma Allah baya sona wallahi na tabbatar yana sona".


"Saboda ya bani abinda mafi yawan masu zagi da aibata ni suna nema amma basu samu ba, kuma gaba ɗaya a cikin littafin Allah da hadisan MANZON ALLAH SAW babu inda aka haramta yin sana'a. Ni rawa da waƙa sune jari na".


Modern Journalists!

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post