Wata Kutun majastiri a Akure babban birnin jihar Ondo ta garkame wani matashi mai shekaru 31 mai suna Dele saboda samunsa da laifin kashe wata mata tsabar Jima'i
Masu karan sun ce Dele bai saurarawa matar ba ya zakke mata a gado har sai da yaga ta daina motsi. Duk kuwa da ihun da ta rika yi na ta gaji ya kyaleta hakan amma yaki.
Lauyar wanda ake kara C.O Falana dai ya nemi a bashi damar bada belin wanda ake tuhumar kamin ya gabatar da shedunsa.
O.R Yakubu mai shariya ya inginza keyar Dele zuwa gidan maza. Inda ya daga karan zuwan gobe 14 ga wannan watan da muke ciki
Daga Abdul Tonga