Neman Duniya: Ya Kashe Uwarsa Yayi Zina Da Gawarta Saboda yai Kudi


Wani yaro dan shekaru 18 da haihuwa mai suna Samuel Akpobeome daga jihar Delta. Yaron yace ya kashe uwar nasa ne a lokacin da ta shagala da bacci yasa wuka ya sossoketa har sai da ta daina motsi. 


Daga bisani kuma bayan ya kashe ta sai ya yi lalata da gawar uwar tasa wacce ta tsuguna ta haifeshi tasha wuyar ɗawainiyar sa har ya zama mutum, amma haka ya aikata wannan mummunan aikin akan ta duk saboda wani lakanin samun kudi da wani boka ya bashi.


A lokacin da kwamishinan yan sandar jihar Mr. Johnson Kukoma ya gabatar da masu laifi a gaban manema labarai. Samuel yace Mamansa ba ta yi masa komai ba kuma tana matukar nuna masa kauna.


Amma shawaran da bokan ya bashi na kashe uwarsa yayi zina da ita na kwanaki idan yana son ya zama kamar Dangote, shine yasa yayi hakan. Wanda kuma daga baya nake yin nadama akan wannan mummunan aikin da na aikata, cewar matashin.


Ko a satin da ya gabata ma ankama wani mutum da laifin kwakulewa wani matashin yaro idanu domin ya kaiwa wani boka da zai yi musu layar yin bata a Ningi dake jihar Bauchi.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post