Na Sadaukar Da Raina Ga Kasata Najeriya | Cewar sojan da ya rasa ransa a hannun ƴan bindiga a shiroro


Ɗaya daga cikin sojojin da ‘yan bindiga su ka kashe a harin wurin haƙar ma’adinan Ajata-Aboki da ke yankin Shiroro a Jihar Neja, ya ce ya sadaukar da ran sa ne domin Najeriya ta samu zaman lafiya.


A cikin wani faifan bidiyon da aka watsa watanni kaɗan kafin kai harin, an nuno sojan mai suna Husseini Muhammad ɗan asalin Jihar Jigawa, ya roƙi ‘yan Najeriya su yi wa sojojin su da ke bakin daga addu’ar samun nasarar samar da zaman lafiya a ƙasar nan.


“Yauwa abokai na da masoya na, iyaye na da kowa da kowa. Ga mu nan a cikin surƙuƙin dajin Minna, ina ‘yan bindiga ke fatattakar mutanen ƙauyuka. Tuni har mun dira wurin.


“To mu na buƙatar addu’o’i daga gare ku. Mun sadaukar da rayukan mu don kare rayukan jama’a, iyalan su da ƙasa baki ɗaya. Mun zo nan domin mu ceto su, ko mu dawo ko a kashe mu. Ko da rai ko ba rai.” Haka ya faɗa a cikin bidiyon.


Muhammad ya rasu ya bar mata ɗaya da ‘ya’ya bakwai. Ya na cikin sojoji 30 da ‘yan bindiga su ka harbe.


Jaridar Premium Times Hausa ta rawaito cewa waɗanda ake fargabar sun mutu kimanin mutum 43 ne, waɗanda su ka haɗa da sojoji 30 da mobal 7, an kuma tabbatar da ɓacewar wasu jami’an tsaron a gumurzun su da ‘yan ta’adda a daji haƙar ma’adinan da ke Ajata-Aboki, cikin Ƙaramar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post