Burina Kawai NA Kashe Mutane Ni Bana Yin Garkuwa Da Su, Cewar Shugaban 'Yan Ta'addan Zamfara Aliero


Shahararren sarkin ‘yan bindiga, Ada Aleru, wanda a kwanan nan aka yi masa nadin sarautar Sarkin Fulanin Yandoton Daji (shugaban Fulani a Yandoton Daji) a wani ikirari mai ban tsoro da yai , ya ce ba ya sace mutane sai dai ya kashe su.


Nadin sarautar Aleru, wanda shi ne jagoran ‘yan ta’adda a yankin Tsafe da Faskari da jahohin Zamfara da Katsina, ya jawo ce-ce-ku-ce a fadin kasar nan.


Gwamnatin Katsina za ta bayar da tukuicin Naira miliyan 5 ga duk wanda ya ba da bayani kan inda za'a da kama Aliero , wanda ake zargi da kashe mutane 52 a garin Kadisau da ke karamar hukumar Faskari a shekarar 2019.


A hirarsa da aka yi dashi da manema labarai,  Aliero ya shaida wa BBC cewa ya fusata da Hausawa da gwamnatin Najeriya. 


A cikin wani shirin mai taken “Mayaƙan Yan Bindiga na Zamfara” da aka ce za a nuna a ranar 25 ga Yuli, 2022, Mista Aleru ya ce yayin da mutanensa ke garkuwa da mutane, shi kuma yana da sha’awar kashe mutane ne kawai.


Ko da dan jaridar yake tambayar sa cewa idan kun yi garkuwa da mutane gwamnati tana cewa ba ta biyan ku Ko sisi, sai dai Aliero ya karyata hakan inda yake cewa idan sun kama mutane sai gwamnati ta biya su miliyan 60 kafin su sake su. 


Ko da aka tambayi Aliero me yake yi da kudin ya bayyana cewa suna Kara siyan makamai ne ragowar kudin kuma su yi bukatun su. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post