Matakan Da Mutane Ya Kamata Su Ɗauka Domin kare Kansu Daga Masu Yin Kutsen Akawun (Hackers)



A wannan lokacin mutane da dama suna fuskantar matsaloli game da yadda ake yi musu kutse a akawun ɗin su irin su facebook, twitter, Instagram da sauransu. Wasu sunanan suna bibiyar yadda za suyi su mallaki wasu bayanan ka domin su yi maka kutse.


To akwai hanyoyi da dama da za ku iya amfani dasu wajen kare kanku daga masu son yi muku kutse. Ga wasu daga cikin hanyoyi 5 da za kuyi amfani dasu ku kare kanku kamar haka;



1. Da farko kada ku yarda ku saka lamban wayarku ko sunan garin ku ko sunan ƙauyen ku kaɗai a matsayin "Password" a Facebook ko Instagram ko Twitter. Misali: Yahaya,Bauchi,Wase,KanoState. Ko: Fatima,Habiba,Medile,Hotoro,0803060099,8030600,30600979.


2. Kada mutum ya saka "Password" da wani abu da ya shafi bayanansa na shafin facebook.

Misali: Suna na Yahaya sai na saka password ɗina a matsayin "YAHAYA YAHMIS" ko "YAHAYA123" ko yahayayahmis123 da makamancin wannan.


3. Mutum ya saka " Password" mai wahalar gaske da ya haɗa abubuwa da yawa kamar: Harufa (Alphabets) Babban baƙi (A - Z) da Ƙaramin baƙi (a - z) da Lambobi (0 - 9) da  Symbols (@,#,$,%,-,?,*,£,=) da sauransu. Misali: "Il0v3U_100%@Masoyiyata" = (I Love you 100% Masoyiyata) da sauransu.


4. Mutum yayi activating ɗin "Two-factor authentication (2FA)". Wanda zai taimaka ta yadda babu wanda zai shiga account din ka ko da ya san password da username din ka dole sai yana da "2FA Code" din da aka tura a lambar wayar da aka yi amfani da "Two-factor authentication (2FA)" dashi ko kuma ta cikin manhajar (Authy ko Google Authenticator) da aka saita da shi kafin a iya buɗewa.


5. Abu na ƙarshe shine; ayi activating ɗin "LOGIN ALERT" wanda zai sanar da ku duk lokacin da akayi ƙoƙarin bude shafinku na Facebook da na Instagram da na Twitter ɗin ku. Za'a turo muku da saƙo da cewar "wani mai waya kaza da kaza daga waje kaza yayi ƙoƙarin buɗe account ɗin ku, shin ku ne?" daga nan ko kuce kune ko kuce baku ba ya danganta ga abunda kuke son kuyi a lokacin.


Wadannan sune kaɗan daga cikin hanyoyi da zamu iya kawo muku su a wannan rubutun da za su taimaka muku wajen tsare akawun ɗin ku daga faɗawa hannun masu yin kutse wato Hackers.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post