Ƴan ta'adda sun sace ƴan kasuwa fiye da 40 a hanyar Zamfara|Android PolsRahotanni daga Jihar Zamfara na cewa wasu ƴan ta’adda da ake zaton ƴan fashin daji ne, a ranar Asabar sun yi garkuwa da mutane kusan su 40 a hanyar Sokoto zuwa Zamfara. Mafi yawan waɗanda lamarin ya rutsa da su ƴan kasuwa ne masu safarar wayoyin hannu da sauran kayayyaki masarufi a Kasuwar Bebeji da ke jihar Zamfara.


Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun tare matafiya sama da 60 da suke dawowa daga Ƙaramar Hukumar Tambuwal a jihar Sokoto amma 20 sun yi sa’ar tserewa daga harin. Shugaban kungiyar ƴan kasuwar, wanda ya tabbatar wa gidan jaridar BBC Hausa harin yace, lamarin ya faru ne a kusa da Kureka da ƙauyen Bakura.


Ya ce kimanin mutane 40 ne ke cikin wata motar bas ta Coaster, yayin da 18 daga cikinsu ke cikin wata motar ƙirar Hiace. Kakakin Rundunar Ƴan Sandan Jihar Zamfara SP. Muhammad Shehu ya tabbatar da faruwar harin, ya ce ana ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro na haɗin gwiwa domin gano inda a ka kai ƴan kasuwar da kuma kubutar da su.


Jihar Sokoto da Zamfara dai sun daɗe suna fama da hare-haren ƴan bindiga wanda ake yin garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa. Sai dai haryanzu gwamnatin jihohin na iƙirarin cewa suna ɗaukar matakai domin shawo kan lamarin.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post