Ga Wata Sanarwa Ga Duk Mai Yin Amfani Da Manhajar WhatsApp Ta GB


Barknmu da saduwa da ku a wannan filin na fannin fasaha inda a yau za ku ji wasu muhimman abubuwa da Yakamata duk wani mai yin amfani da GB Whatsapp ya sani don mutum ya  kare kansa daga faɗawa cikin matsala.


Domin a wannan lokacin akwai dubban mutane wanda suke yin amfani da manhajar GB Whatsapp saboda irin tsare-tsaren da ya zo da shi sun sha bambam da sauran manhajar asali ta Whatsapp. Shi dai GB Whatsapp ba  kamfanin Whatsapp na asali bane suka ƙirƙire shi ba.


Domin shi ya zo da wani sabon salo iri-iri wanda na asali ba shi da su misali, yana ba da damar ajiye hoto, bidiyo ko kuma yin kwafar rubutu daga status ɗin mutum kai tsaye. Sannan kuma yana da alamu irin na ɓoye alamar karantarwa ko kuma karɓar saƙo ko kuma ya nuna alamar idan mutum yana kan network da dai sauran abubuwa.


A taƙaice dai manhajar GB Whatsapp na ɗauke da wasu tsare-tsare wanda shi ainihin WhatsApp ba shi da su, wannan dalili yasa mutane suka fi son sa da kuma yin amfani dashi kai tsaye ba tare da sanin wasu illoli da yake dasu ba wanda kan iya haifar da matsalar fitar da bayanan duk mai amfani dashi.


Kamar dai yadda masu bincike kan manhaja suke bayyana wa cewa shi wannan manhajar ta GB Whatsapp yana ɗauke da wasu bayanai da masu yin kuste suke yin amfani dashi wajen ganin bayanan ku da suke kan wayar ku da kuma layin da kuke amfani dashi a manhajar. Shine dalilin da yasa suka tsara shi domin ɗauke hankalin duk wanda yake son yin amfani dashi.


Don haka duk mai yin amfani da wannan manhajar ta GB Whatsapp muna mai baku shawara da ku ƙauracewa yin amfani dashi saboda wasu dalilai da aka bayyana cewa yana da illa domin za su iya yi muku kutse su sace muku kuɗi ko wani abu makamancin haka. 


Ga dai wasu daga cikin dalilan da ya kamata ku sani idan kuna amfani da wannan manhajar Kamar haka;


(1) Manhajar GB Whatsapp ba na kamfanin Whatsapp na asali bane wasu taron mutane ne da ake kira da Alex Mode suka ƙirƙire shi ba tare da lasisi ba, kuma sun saɓa tsarin ƙirƙira da bayar da lamunin amfani da sirrikan jama'a. Shi yasa ko adirshi ɗin su ba zaka gani ba ta yanar gizo-gizo.


(2) Duk mai yin amfani da wannan manhajar ta GB Whatsapp ya sani cewa duk wasu bayanan ku da suke kan wayar ku za su iya ɗiban su ba tare da kun sani ba, domin idan kana amfani da manhajar babu wani abu da ke cikin wayarka da ba za su iya gani ko su ɗauka ba.l


(3) Rashin tsaro, domin duk abinda kake yi a manhajar GB Whatsapp ana ganin ka tamkar tsirara duk wani sako da ka tura ko kuma ka karɓa to ana ganin sa domin ba ta da sirri, shi yasa babu wuya ayiwa mutum kuste a cikin sa. Ko a kwanakin baya akwai wata mata da akaiwa kuste aka ringa turawa ƴan uwan ta saƙonni inda aka damfare su manyan kuɗi.


(4) Inda zaka gane cewa ita wannan manhajar ta GB Whatsapp ba halattacciya bace idan za ka ɗauko shi daga yanar gizo-gizo za ka ga suna yi maka gargaɗin cewa wannan manhajar za ta iya cutar da kai ko kuma bayanan ka. Shi baka taɓa lura da hakan ba, idan kuwa har kana ganin haka don mene za kasa kanka cikin halaka.


(5) Wannan manhajar ta GB Whatsapp ba ta yin 'backup' wato dawo da bayanan ka, domin ta saɓawa kamfanin Google, kuma shi dawo da bayanai baya yuwa sai Mutum yanada rajista da kamfanin Google. Shine yasa idan ya lalace sai kaga mutum ya rasa dukkan bayanan sa.


Da fatan wannan saƙon zai isa ga dukkan mai yin amfani da wannan manhajar ta GB Whatsapp. Kuma ina fatan zaku turawa sauran jama'a domin su amfana.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post