Za'a Fara Yin Amfani Da Fasahar 5G A Najeriya A watan Agusta Na 2022


Hukumar Kula da Ayyukan Sadarwa ta Kasa (NCC) ta bada sanarwar cewa tana gab da fara yin amfani da Sabuwar fasahar sadarwa ta (5G) a Najeriya inada hukumar ta bayyana sunayen kamfanoni biyu wato MTN da kuma Mafab a matsayin waɗanda zasu fara yin aiki da sabuwar fasahar sadarwa ta 5G a ƙasar.


Hukumar ta (NCC), a hukumance ta bayyana cewa a wannan shekara ta 2022 ne cikin 24 ga watan Agustan wannan shekara a matsayin ranar da kamfanonin za su fara amfani da sabuwar fasahar ta 5G.


Shugaban Hukumar ta (NCC) Farfesa Garba Danbatta a wata hira da yai da gidan Radio na BBC Hausa ya shida musu cewa sun kammala duk tsare-tsaren da suka kamata wajen fara yin amfani da fasahar da suka haɗar da bayar da lasisi ga kamfanonin da za su samar da fasahar a faɗin ƙasar. 


Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya zanta da Adamu Garba, na kamfanin IPI Solutions Group wanda yak ware a fannin ayyukan sadarwa, wanda da ya fara da yi masa bayani game da abin da ake nufin 5G.


Duk da cewa za a fara aiwatar da Fasahar ne daga manyan biranen jihohi kuma sannu a hankali za a ƙara zuwa wasu yankuna a faɗin jihar, yana da kyau a fahimci cewa, shi wannan sabon Tsarin sun banbanta da hanyar sadarwa ta 1G, 2G, 3G da 4G, Kuma fasahar ta 5G za ta kawo ingantuwar hanyoyin sadarwa da yawa, gami da saurin sadarwa mai girma, a cewar Farfesa Umar Garba Danbatta.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post