Na Gaji Da Zaman Gidan Iyaye Na, Aure Nake So Da Duk Wanda Ke Sona Yazo Muyi Aure, Cewar MaryamWata matashiya mai suna Maryam ta bayyana takaicin ta dangane da halin da ta tsinci kanta na rashin aure, inda ta bayyana cewa bata san zaman gidan iyaye bala'i bane sai a lokacin watan Azumi Ramadan.


Maryam ta ce ta girma amman abin kunya da takaici a kullum da ita da sauran ƙannen ta suke yin rububin kokawar karɓan kayan shan ruwa da sauran kayan buɗa baki kamar Kunu da ƙosai.


Maryam ta ce ta gaji da ganin irin wannan wulaƙanci, don haka tace a shirye take da ta yi aure ga dukkan wanda Allah ya kawo mata indai zai so ta tsakani da Allah, to a shirye take da ta yi aure.


Ƴan mata dai a wannan zamanin suna nuna damuwar su game da rashin aure, hakan na faruwa ne a dalilin rashin samun mazaje tsayayyau da za su aure su. Sai dai hakan na faruwa ne sakamakon su Samarin rashin kuɗin auren.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post