Mayaƙan ISWAP sunkai wani Sabon hari a Jihar Borno


Wani rahoto ya bayyana yadda mayaƙan ƙungiyar ISWAP masu iƙirarin jihadi a Yammacin Afirka, suka kai wani sabon hari a wani ƙauye da ke kusa da Karamar Hukumar Chibok, inda aka aka sace ɗaliban makarantar sakandaren Chibok a Jihar Borno.


Wata majiya ta ƴan sa-kai ta shaida wa Jaridar Aminiya cewa mayaƙan sun kai harin ne a ƙauyen Kautakari da ke da tazarar kilomita 15 tsakaninsa da garin Chibok, inda suka fara harbe-harbe kan mai uwa da wabi tare da cinna wa gidaje wuta. Gabanin faruwar wannan hari sai dai mayaƙan suka tarwatsa wani sasanin dakarun soji a yankin Kada da ke da tazarar kilomita 2 kacal tsakaninsa da kauyen Kautakari.


Majiyar ta ce mayaƙan sun biyo dare ne ta cikin sahara, inda suka fara harbe-harbe daga kowace kusurwa babu ji ba gani. Kawo yanzu haka duk mazauna ƙauyen da sojoji sun gudu cikin daji, wasunsu kuma sun fake a garin Chibok” a cewar majiyar.


Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa wannan hari na zuwa ne a daidai lokacin da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutterres yake kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu a Najeriya, inda a ranar Talata ya ziyarci Jihar Borno domin ganawa da gwamnan jihar Babagana Zulum.


Babban Jami’in na Majalisar Dinkin Duniya ya je Maiduguri, babban birnin Jihar Borno a ranar Talata inda ya gana da Gwamna Babagana Umara Zulum, da kuma iyalan mutanen da rikicin Boko Haram ya yi sanadin rasa rayukansu. Hazalika Sakatare Janar ɗin ya gana da shugabannin addinai da na ƙungiyoyin mata da matasa da kuma shugabanin kamfanoni masu zaman kansu.


Baya ga waɗannan mutane da ya gana da su, ya kuma gana da jami’an difilomasiyya da ma waɗanda ke sansanonin ƴan gudun hijra a Jihar Borno. Kawo zuwa wannan lokacin babu wani rahoto dake bayyana adadin mutanen da suka rasa rayukansu a yayin kai harin.


A ƴan kwanakin nan dai ayyukan mayaƙan ISWAP ƙaruwa yake yi inda suke cigaba da kai hare-hare. Sai dai kuma a satin da ya gabata haɗakar sojojin Najeriya da ƙasar Kamaru sun kai wani farmaki a tafkin Chadi inda suka hallaka mayaƙan ISWAP ɗin da dama.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post