Matsalar Rashin Tsaro Na Ƙara Samun Cigaba A Jihar Sokoto


A Najeriya, musamman a arewacin ƙasar matsalolin rashin tsaro na ci gaba da hana jama'a barci da ido biyu rufe; wasu saboda fargabar abin da ka iya zuwa ya dawo, ko abinda zai faruwa cikin dare, wasu kuwa don tsaron rayuka da dukiyoyinsu da na al’umma da kuma gidajen su da Iyalin su.


Irin wannan al'amari na rashin tsaron ne ya faru a garin Takakume da ke cikin ƙaramar hukumar Goronyo a jihar Sakkwato, inda wasu da ake zargin ɓarayi ne suka afka wa jama'a, su ka tarar da su farke, aka yi bata-kashi tsakaninsu.


Lamarin rashin tsaron dai yana ci gaba da ta'azzara, inda ake ci gaba da samun asarar rayukan jama'a a sassa daban-daban na Najeriya, musamman ma dai a arewacin ƙasar wanda kullum lamarin tsaro sai ƙara lalacewa yake yi.


Mazauna garin Takakume da ke karamar hukumar Goronyo a jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya, da daren ranar asabar, sun ɗauki baƙuncin ƴan bindiga, waɗanda suka afka musu, sai suka tarar da jama'a a farke, daga nan suka soma musayar wuta.


Shugaban karamar hukumar ta Goronyo, Abdulwahab Yahaya Goronyo, wanda da shi ne aka yi Jana'izar mutane 7 da aka kashe a ɓangaren mutanen garin na Takakume, ya ce yanzu ƙura ta lafa a yankin. Ƴan Najeriya dai na ci gaba da kira ga mahukunta da su ƙara yin azama koda za'a shawo kan wannan matsalar da ta addabi jama'a.


Jihohin Sokoto, Zamfara, da Katsina suna fuskantar matsalolin tsaro wanda kusan kullum sai kaji ƴan bindiga suna kai hare-hare wanda ke sanadin mutuwar mutane da dama tare da asarar dukiyoyi. Duk kuwa da iƙirarin da mahukunta suke yi cewa suna ɗaukar matakai domin kawo ƙarshen lamarin.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post