Ƙarfin Ruwan Sama Yai Sanadin Mutuwar Mutane Biyar A Garin Damaturu Na Jihar Yobe


A ƙalla mutane biyar ne suka rasa rayukansu yayin da fiye da 30 suka jikkata biyo bayan wani ruwan sama da aka tafka kamar da bakin ƙwarya haɗe da iska da guguwa a garin Damaturu babban birnin Jihar Yobe.


Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar SEMA ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta bayyana cewa gidaje fiye da 100 ruwan ya tafi dasu sakamakon saukan ruwan saman. Mohammed Goje wanda shine sakataren SEMA yace sun samu rahoton faruwar iftila'in.


Wanda hakan yasa suka taimaka wajen gaggawar kai waɗanda suka jikkata zuwa asibiti. Goje ya tabbatar da cewa mutane biyar ne suka rasa rayukansu daga cikin 41 da guguwar ta rutsa dasu, kuma mutanen sun fito ne daga yankuna daban-daban a birnin Damaturu inda aka kaisu zuwa asibiti.


Unguwannin da lamarin ya shafa sun haɗa da Abbari Extension, Waziri Ibrahim Extension, Pompomari, Gujba road da rukunin gidajen ƴan majalisun dokokin jihar da sauran wasu guraren da har kawo zuwa haɗa wannan rahoton ba'a gama bayyana su ba.


Ko a shekarar bara ma an samu ambaliyar ruwa a wasu sassa daban-daban na Najeriya wanda hakan yai asarar rayuka da dukiyoyi. Sai dai masu sharhi na kira da mutane da a gyara magudanar ruwa da hanyoyi domin samun hanyar ruwa hakan zai rage ambaliyar ruwa.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post