Idan Bakaso Matarka Ta Raina ka Karkayi Waɗannan Abubuwan A Gabanta



A'uzu billahi minasshaidanirrajim bisimillahir rahmanirrahim! Wasallahu Ala Nabiyyina Muhammad wa'ala-alihi wasahbihi ajima'in, Wa-man tabi'ahum bi ihsanin ila yaumiddin wa-ba'ad.


Barkanmu da sake saduwa daku a wannan lokacin a cikin cigaba da shirye_shiryen da muke kawo muku. 


Yau insha Allah zamuyi magana akan wasu abubuwa da maza suke yi a gaban matan su wanda hakan ke jawo matar tanan raina mijin. 


Waɗannan abubuwan wasu mazan ba su ɗauke shi a matsayin wani abu ba, sai dai hakan yana jawo raini a wajen matarka. Don haka dole maza su kiyaye su. waɗannan abubuwan sune Kamar haka gasu zamu liassafo :


(1) Hutu Ko tusa;

Bai kamata kuna tare da iyalin ka ace Kasaki tusa ba hakan ba ƙaramin raini yake jawo maka wajen iyalin ka ba. Kamar yadda itama ba'a so tayi hakan a gaban mai gidan. 


(2) sai abu na biyu kuma shine yin susa;

Bai kamata miji idan ƙaiƙayi yana damun sa yaita so sawa a gaban iyalin sa ba musamman ƙaiƙayin matse-masti. Yin hakan yana nuna wawanci da gaɓanta, Idan susar jiki ne wannan ba matsala bane don ka sosa a gaban iyalin ka zaka iya cewa ma ta sosa maka, amma susar matse-masti a gabanta ba daidai bane. 


(3) Shan sigari (taba); 

Shan sigari a gaban iyali yana Ƙara zubar da mutunci matuqa gaya a gaban iyali koda tasan cewa kana sha to karka kuskura ka ringa sha a gaban iyalin ka musamman ace idan kanada yara, akwai magidanta da yawa da suke shan sigari wanda iyalin su ma sun sani amma basa sha a inda iyalin su zasu gani sai sun keɓe. 


(4) Ba'a so namiji ya ringa yin zagi (ashar) a gaban iyalin sa; 

Wani namijin sai kaga ga yara ga mata amma idan yana zagi kamar wani bamaguje, Idan anyi masa laifi a gidan Ko kuma daga waje a kaimasa laifin sai yazo gaban iyalin yaita ƙundunma ashar. Hakan ba daidai bane, a matsayin ka na uba abin koyi bai kamata aji kana ƙunduma ashar a gaban iyalinka ba domin zai rage maka mutunci zai rage maka ƙima a idanun su. 


(5) Abu na gaba shine bai kamata namiji ya balbale matar sa da fada ba a gaban ƴaƴan ka ba, duk wani abu da yai zafi sai kabari sai gaka ga ita sai kai mata duk faɗan da zakai. Amma yiwa matar ka faɗa da zagi a gaban ƴaƴan ka hakan yana zubar maka da ƙima da raini wajen ƴaƴan naka, kuma hakan kana koya musu mummunar tarbiyya da ɗabi'u marasa kyau. Domin su yara abinda suka ga iyaye suna yi suma shi sukeyi. Don haka dole iyaye su kiyaye abubuwan da zasu yi a gaban ƴaƴan su. 


(6) Ƙarya; 

kada ka kuskura ka zamo mai ƙarya a gaban iyalinka, misali idan ankira ka a waya a gaban iyalinka zakai ƙarya a gaban su gasu suna kallon kana ƙarya wannan shima yana zubar da girma da mutunci gaya a wajen iyalinka wajen ganin cewa kai ba mutumin kirki bane, Ko kuma azo neman ka ka tura yaran kace baka nan kaga kayi ƙarya ƙiri-ƙiri. Don haka yin wannan bai kamata ba, ya kamata mazaje su san haka. 


Wannan sune kadan daga cikin abubuwan da bai kamata miji yaiyi su a gaban iyalinsa ba. Domin aikata su yana zubar da ƙima da darajar maigida a wajen iyalinsa. Da fatan za'a kula kuma a kiyaye. Nan gaba zamu ɗora akai Sannan suma mata zamu kawo nasu abubuwan wanda bai kamata suyi a gaban mazajen su ba. 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post