Cikin Jerin Musulmi 500 Masu Daraja A Faɗin Duniya Shugaba Buhari Shine Yazo Na 16


kamar yadda cibiyar nazarin addinin Islama dake Oman a ƙasar Jordan suka fitar da jerin musulmi masu daraja a faɗin duniya, cikin su har da shugaban Najeriya Muhammad Buhari wanda shine na 16 a cikin fitattun musulmi masu faɗa aji a faɗin duniya.


Kusan duk shekara cibiyar tana wallafa sunayen fitattun musulmai guda 500 da suka shahara kuma suke da ƙarfin faɗa aji a faɗin duniya. Kuma a bana bincken da cibiyar ta wallafa karo na 12 ta ce Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari shine na 16 a jerin musulmi masu ƙarfin fada aji a duniya.


Musulmi na farko mai faɗa aji a duniya shine Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, wanda yake musulmi mafi ƙarfin faɗa a aji a duniya. Sai kuma mai biye masa Sarki Salman na ƙasar Saudiyya. Sai kuma na uku, Jagoran Iran Ayatollah Ali Khamenei a cikin jerin musulmi masu karfin faɗa a ji a duniya.


Cibiyar ta bayyana cewa yawan musulmi a faɗin duniya a wannan shekarar ta 2022 yakai kimanin biliyan 1.9, wato kaso 26 na yawan al’ummar duniya. A cikin jerin fitattun musulmi masu daraja a duniya, babban Shehin Malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Ibrahim Saleh Maiduguri shine  yazo na 48 a duniya.


Sauran ƴan Najeriya da ke cikin jerin musulmi masu karfin fada a ji a duniya sun haɗa da Sarkin Musulmi Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar III da Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero. Akwai kuma Shehin malamin Tijjaniya Sheikh Dahiru Usman Bauchi da jagoran ƙungiyar Shi’a ta IMN Malam Ibrahim Zakzaky da kuma attajirin Afrika Alhaji Aliko Dangote.


Suma masu buga ƙwallon ƙafa ba'a barsu a baya ba, cikin sunayen musulmai 500 mafi ƙarfin faɗa aji a duniya sun haɗa da ƴan ƙwallon kafa inda cibiyar ta bayyana ɗan wasan ƙasar Masar da ƙungiyar Liverpool Mohamed Salah a matsayin na 42 cikin jerin fitattun musulmi a faɗin duniya.


Sauran ƴan ƙwallon da ke cikin jerin sunayen sun haɗa da ɗan wasan ƙasar Senegal da Liverpool, Sadio Mane da Paul Pogba ɗan ƙasar Faransa sai kuma Zinedine Zidane, wanda shima ɗan ƙasar Faransa ne.


Sai dai a ƙarshe cibiyar ta ce zaɓen waɗannan mutanen ba ya nufin nuna goyon baya ga aƙidunsu ko amincewa da ra’ayinsu bane, illa kawai auna girman ƙarfin faɗa aji da suke da shi a faɗin duniya.


Sai dai wasu masu sharhi suna ganin cewa akwai manyan musulmi wanda suke da ƙarfin faɗa aji a faɗin duniya da ya kamata ace an saka su a cikin wannan jerin, kamar irin su tsohon Sarkin Kano Muhammad Sunusi na 2. Da irin su Sheikh Mahi inyass na ƙasar Senegal, Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass da sauran su.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post