Domin Mata: Hanyoyi 7 Da Zaki Gane Nagartaccen Namiji


Yana da kyau duk wata mace tasan waɗannan abubuwan domin sanin su yanada muhimmanci. Hakan zai taimaka mata tasan irin kalar namijin da za ta zauna dashi. Domin ba duka maza ne suke da irin wannan ɗabiun ba sai kaɗan daga cikin mazaje.


Waɗannan wasu ne daga cikin hanyoyin da zaki gane cewa kin dace da nagartaccen namiji, wanda zaku gudanar da rayuwar aurenku cikin kwanciyar hankali tare dashi, babu wanda zaiyi nadamar kasantuwa da wani acikinku. 


Ga dai wasu daga ciki halayane nagartaccen namiji guda 7 da zamu iya kawo muku a wannan lokacin:


(1) Namijin da zai sanya ki yin farin ciki a koda yaushe kuma a kowane yanayi. 

(2) Namijin da yake neman halaliyarsa, wanda yake gudun haram. 

(3) Namijin da yake sonki domin Allah, ba don wani abu daga jikin ki ba. 

(4) Namiji wanda zai jiyar dake tsoron Allah a kowane hali. 

(5) Namijin da zai kusantar dake ga Allah, da kuma bautar sa. 

(6) Namijin da zai ciyar dake halaliyarsa, wanda Zaiji tsoron ciyar dake haram. 

(7) Namijin da zai kiyaye haƙƙin aurenku, da sauke nauyin da Allah ya dora masa akan ki.


"Abu ne mai matuƙar wahala mace ta sami namijin da ya haɗa waɗannan sifofin kuma tayi nadamar kasancewa dashi a rayuwarta"


"Abin mamaki! wai yanzu ya zama ƙauyanci ga wasu mazajen wannan zamanin su bayyanar da fara'a da wal-wala ga matansu, babu wasa a tsakaninsu saidai ɓacin rai, da zarar ya shigo gida ko sallama bazai yi mata ba, sai dai yayi mata gyaran murya ya shige kawai, babu tausayi ballema ya zame mata nagartaccen namiji, subhanallah! Allah ya kyauta" ya kamata maza a gyara. 


Kuma kema matar ki kula da duk wasu abubuwa wanda zaki ya jawo hankalin sa kuma ki kiyaye abubuwan da zasu jawo ɓacin ransa. Domin wasu lokutan matan sune suke jawo mazajensu suna canja dabi'u.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post