Bayan tantancewa da bincike mai zurfi Maulanmu Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya tabbatar da an ga jaririn watan Shawwal a jihohi kamar jaka Birnin Tarayya Abuja, jihar Nasarawa da kuma Kurgwi dake jihar Filato.
Ƙarshe dai Maulana Sheikh ya bada umarni a sha ruwa gobe Lahadi babu Azumi Insha Allahu, domin Azumin bana ya zo karshe.
Maganan Sallan Idi kuwa Shehu ya ce tunda nafila ce a dakata sai ranar da za a yi na gari gaba ɗaya sai a yi tare.
Sarkin Musulmi dai ya bada sanarwar cewa ba'a ga watan Shawwal ba wanda hakan ke nuna cewa azumi 30 za'ayi, wanda hakan ya nuna ranar Litinin za'a yi sallah.
Rahoto Daga shafin Rariya